An kara samun masu korona a nigeria.

 Hukumar daÆ™ile cutuka masu yaÉ—uwa a Najeriya NCDC ta ce adadin mutanen da annobar korona ta harba a Æ™asar sun kai 62,853


bayan da aka gano ƙarin mutum 162 da suka kamu da cutar ranar Asabar.

Adadin mutum 58,675 sun warke kuma an salleme su, yayin da 1,144 suka kwanta dama zuwa yanzu.

Jihar Legas ita ce mai adadi mafi yawa na mutanen da suka kamu a ranar Jumma'a, da mutum 106, Sai Abuja mai mutum 25 da suka kamu.

Oyo na da mutum 14, Edo da Kaduna kuwa na da mutum 7-7 da suka kamu da koronar a kowacce jiha.

Ogun ta samu mutum 4 da suka kamu, sai Bauchi da Benue masu mutum 2-2.

Jihohin Kano da Osun da kuma Rivers na da mutum dai-dai da suka kamu a kowacce jiha.

Hanyoyi 4 na kare kai daga cutar coronavirus

Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana matakan da mutane za su dauka domin kauce wa kamuwa da cutar numfashi ta coronavirus.

Yaya zan kare kaina daga cutar?

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce:

■ Ku wanke hannayenku da sabulun gargajiya ko sabulun ruwa da ake wanke hannu da shi, wato hand gel, wanda zai iya kashe kwayoyin cuta

■ Ku rufe hanci da bakinku lokacin da kuke yin atishawa da kyallen fyace majina - sannan ku wanke hannayenku bayan kun yi atishawa domin hana kwayoyin cutar yaduwa.

■ Ku guji taba idanunku, ko hanci ko bakinku- idan hannunku ya taba wurin da cutar ta shafa, za ta iya yaduwa zuwa sauran sassan jikinku.

■ Kada ku rika matsawa kusa da mutanen da ke yawan atishawa ko tari da masu fama da zazzabi - za su iya watsa cutar cikin iska ta yadda ku ma za ku iya kamuwa da ita. - akalla ku matsa nesa da su ta yadda tazarar da ke tsakanin ku za ta kai kafa uku.

Post a Comment

Your comment will be directly sent to the website developer.

Previous Post Next Post