Firanministan Burtaniya ya sanar da kakaba dokar hana fita a duk fadin Ingila har tsawon wata daya, bayan bazuwar annobar Korona a karo na biyu.
Boris Johnson ya sanar cewa daga ranar Alhamis duk wata fita da ba ta zama ta dole ba an dakatar da ita.
To amma duk da haka kananan makarantu da kuma jami'o'i za su ci gaba da kasancewa a bude.
A baya Mr Johnson ya yi ta jan kafa wurin daukar irin wannan mataki, to amma a yanzu ya ce ba su da zabi.
To sai dai masu kamfunoni a Ingila sun ce irin yadda bikin Kirsimati ya matse za a gurgunta harkokin kasuwanci za kuma a rasa ayyukan yi.
Karo na biyu kenan a na saka dokar kulle a duk fadin yankin Ingila
Karo na biyu ke nan a na saka dokar kulle a duk fadin ngila
Tuni Ireland ta Arewa da kuma Wales su ka kakaba dokar kulle, kuma a ranar Litinin Scotland za ta kara tsaurara dokar kullen a nata yankin.
A cewar Mr Johnson za a kakaba dokar ne 'a ranar Alhamis har zuwa ranar 2 ga watan Disamba don tabbatar da cewa annobar Korona ba ta ci karfin asibitoci ba'.
A wata mai kama da haka Firanministan ya tabbatar da cewa kullen ba zai shafi gasar kwallon kafa ta Firimiya ba, duk da za a cigaba da bugawa babu yan kallo.
A watan Maris an dakatar da gasar a lokacin kullen farko, daga baya kuma a ka yanke hukuncin dawo wa fagen daga a cikin watan Yuni amma ba tare da yan kallo ba.
Kuma tun daga lokacin a na yiwa yan kwallo gwajin cutar Korona a duk mako.