Mutanen Borno sun yi addu’oi sama da miliyan 41
a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya
domin neman kawo ƙarshen masifar da mayakan
kungiyar Boko Haram suka jefa su a ciki.
Wata ƙungiya ce mai suna Borno Concerned Citizen
wato Æ´an jihar da suka damu da halin da take ciki
ta jagoranci taron addu’o’in a ranar Lahadi.
Barista Zahra Maiduguri É—aya daga cikin waÉ—anda
suka jagoranci addu’o’in ta ce an yi saukar Al
Æ™ur’ani da kuma addu’oi 41, 837,016 domin neman
sauƙin masifar da jihar take ciki.
Daga cikin addu’o’in har da “Istigifari” miliyan
13,669,000 da “Ya LaÉ—ifu” miliyan 10,688,00.
An kuma yi “Ya Kahharu” fiye da miliyan É—aya da
salatin Annabi da kuma salatil fati.
Baya ga addu’u’oin an kuma yanka dabbobin shanu
da nufin yin sadaka domin Allah ya biya buƙata.
Ƙungiyar ta kunshi shugabanni na siyasa da na
gargajiya da malaman addini da malaman Boko a
jihar Borno.
Mayakan Boko Haram sun kwashe fiye da shekara
goma suna kai hare-hare a arewacin Najeriya,
musamman a jihohin Borno da Yobe da kuma
Adamawa.
Hare-haren sun yi sanadin mutuwar dubban mutane
da kana suka raba miliyoyin jama'a da gidajensu.
Harin Zabarmari inda ƙungiyar ta yi wa manoma
yankan rago shi ne hari na baya-bayan nan mafi
muni da Boko Haram ta kai a jihar Borno.