Shugabannin Yarabawa sun yi taron ƙara haɗin
kansu
An kammala taro game da ƙara hadin kan Yarbawa
da kuma kawo ci gaban matasa a wannan shiryar
kudu maso yammaci.
taron da aka gudanar ranar Lahadi ya ƙunshi har da
shugabannin Hausawa da Fulani mazauna yankin
domin neman ƙara haɗin kansu ga samar da tsaro
da zaman lafiya a yankin na Yarabawa
Al'ummar Owu wadanda suka shirya taron sun
tabbatar da cewa dole a tafi da matasa in har ana
neman kawo ci gaba a al'umma.
Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo da
gwamnan jihar Osun Adegboyega Oyetola da
Basarake Oba Adekunle Hammed Makama wanda
ya kira taron sun nemi a raya harkokin al'adu da na
matasa.
Sauran mahalarta taron sun hada da Sarkin Fulani
na jihar Legas, Alhaji Muhammad Abubakar
Bambado II.