An dirka wani malamin coci harsashin bindiga

An harbi wani malamin coci a Faransa
Rahotanni daga Faransa na cewa an harbi wani malamin cocin kibɗawa a birnin Lyon na ƙasar. Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa maharbin ya tsere bayan aika-aikar da ya yi a ranar Asabar. An harbi malamin cocin sau biyu da misalin ƙarfe 4:00 na yammacin ƙasar a daidai lokacin da yake shirin rufe coci. Tuni dai jami'an agaji suka fara yi masa magani a cocin da aka yi harbin sakamakon raunukan da ya samu masu barazana ga rayuwarsa. Ko a ranar Alhamis sai da aka kashe mutum uku a wani hari da aka kai da wuƙa a birnin Nice na ƙasar. Hakazalika kwanaki kaɗan baya sai da wani mahari ya datse kan wani malamin makaranta a ƙasar bayan malamin ya nuna wa ɗalibansa wasu hotunan zanen ɓatanci da aka yi ga manzon Allah, Annabi Muhammad SAW.

Post a Comment

Your comment will be directly sent to the website developer.

Previous Post Next Post