Zaben kasar geneau:

 Mutum 10 sun mutu biyo bayan zaÉ“en shugaban Æ™asa a Guinea

Aƙalla mutum 10 sun mutu sakamakon rikicin da ya biyo bayan zaɓen shugaban ƙasa a Guinea, a cewar ministan tsaron ƙasar.

A yanzu haka Shugaba Alpha Condé ne ke kan gaba a sakamakon da hukumar zaɓe ta sanar daga mazaɓa 14 cikin 20, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

Abokin hamayyarsa Cellou Dalein Diallou ya yi iƙirarin samun nasara kuma ya ce zaɓen na cike da sarƙaƙiya.

Kazalika, ya zargi Shugaba Conde da murɗe sakkamakon zaɓen. Shugaban ya yi kiran da a kantar da hankali.

Sai dai an gudanar da zanga-zanaga da dama tun kafin zaɓen domin nuna adawa da yunƙurin Alpha Conde na sake zama shugaban ƙasa a karo na uku. Amnesty International ta ce mutum 50 ne suka mutu yayin zanga-zangar.

Post a Comment

Your comment will be directly sent to the website developer.

Previous Post Next Post