Laifin kisan Kai :Ana tuhumar malamar makaranta da Laifin kashe dalibanta.

 


Shugabar wata makaranta za ta yi zaman gidan kason shekara 31 saboda mutuwar É—alibai

An yanke wa shugabar wata maranta da yara goma sha tara suka mutu yayin wata girgizar kasa shekaru uku da suka gabata, hukuncin shekara talatin da daya a kurkuku, saboda samunta da laifin kisan kai.

Monica Garcia Villegas ta gina gida a saman makarantar a garin Mexico City.

Ana kyautata zaton cewa nauyin gidan da ta gina a saman makarantar ya taimaka wajen rushewar ginin.

To sai dai Misis Villegas ta dage kan cewa bata aikata wani laifi ba, don haka ma tana shirin daukaka kara.

Hukumomi dai sun ce fiye da mutane dari uku da sittin ne suka mutu a girgizar kasar da ta auku a birnin a shekarar 2017.

Post a Comment

Your comment will be directly sent to the website developer.

Previous Post Next Post