Joe Biden ya tara kuÉ—in kamfe mafi yawa a watan Satumba
Ƙasa da makonni uku a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Amurka, mutumin da ke kalubalantar Trump, Joe Biden, ya sanar da tara kuɗin yaƙin neman zaɓe mafi yawa a watan Satumban da ya gabata.
Gudummawa da É—an takarar na Jam’iyyar Democrat ya samu a wata guda ta haura dala miliyan É—ari uku da tamanin.
Shi dai kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaba Donald Trump bai fitar da sanarwar abin da ya tara ba har kawo yanzu. Amma bai kai na Biden ba a watan Agusta.
Shugaba Trump ya gudanar da yaƙin neman zabensa karo na uku a cikin kwanaki uku, bayan jinyar da ya yi a asibiti a farkon wannan wata sakamakon kamuwa da cutar korona.
Trump ya yi jawabi ga dubban magoya bayansa a Iowa, inda kuri'ar jin ra'ayin jama'a ke nuna cewa za a iya kai ruwa rana.