Jamus ta samu adadi mafi yawa na mutanen da suka kamu da korona
Jamus ta samu adadi mafi yawa na mutanen da suka kamu da cutar korona tun bayan bullarta a ƙasar.
Fiye da mutane dubu shida da dari shida aka bada rahoton sun kamu cikin awanni ashirin da hudu.
Wannan na zuwa ne sa’o’i bayan da Shugabar Gwamnatin Æ™asar Angela Merkel, ta ce za a tsaurara matakan kulle a wasu yankuna don hana cutar bazuwa.
Matakan sun hadar da hana fita da rufe wuraren shan barasa da kuma hana taruwar jama'a.
A makwabciyarta wato Faransa, samun mutun dubu ashirin da suka kamu da cutar a rana guda ya tilasta wa shugaba Emmanuel Macron sanya dokar hana yawon dare a birnin Paris da wasu biranen takwas daga ranar Asabar.
Shugaba Macron kenan ke cewa ina takatsantsan, domin abin da muka gani a baya ya nuna cewa ba komi ne za mu iya shawo kan shi ba.