An soma yaƙin neman zaɓe a Ivory Coast
A yau Laraba ake soma yaƙin neman zaɓe a Ivory Coast gabannin zaɓen shugaban ƙasar da za a yi a karshen wannan wata.
Jam’iyyun adawa na ci gaba da yin kira ga jama'a su amsa kiran fitowa zanga zanga, don daÆ™ile aniyar shugaba mai ci Alassane Ouattara ta yin tazarce a karo na uku.
Dubban mutane sun yi zanga-zangar adawa da wannan matakin a babban birnin kasuwanci na Abidjan, a ranar Asabar.
An hana Æ´an takara hudu na manyan jam'iyyun adawa shiga zaben.
Mista Ouattara ya zama shugaban Ivory Coast me shekaru goma da suka gabata, yayin wani zaɓe mai cike da kace-nace.