End Sars: Rundunar Soji ta gargaÉ—i masu son jawo rikici a wajen zanga-zanga
Mintuna 26 da suka wuce
An shafe kusan mako guda ana zanga-zangar nuna adawa da muzgunawar da Æ´an sanda ke yi wa jama'a a wasu biranen Najeriya
Rundunar sojin Najeriya ta fitar da wani gargaÉ—i ga ''masu son jawo rikici'' su dakatar da jerin zanga-zangar da aka shafe kusan mako guda ana yi kan muzgunawar Æ´an sanda.
Gargaɗin na zuwa ne a yayin da wasu mutane da ba a san ko su waye ba suka kai wa masu zanga-zangar hari ɗauke da adduna a Abuja, babban birnin ƙasar.
An shafe kusan mako guda ana zanga-zangar nuna adawa da muzgunawar da Æ´an sanda ke yi wa jama'a a wasu biranen Najeriya.
An ci gaba da yin zanga-zangar duk da cewa hukumomi sun amince su rushe runudar ta SARS da ke yaƙi da fashi da makami.
Mai magana da yawun rundunar Kanal Sagir Musa a wani saƙo na Facebook, ya wallafa cewa "Rundunar soji na gargaɗin duk wasu masu son tayar da tarzoma da su dakatar da abin da suke yi, a yayin da take aiki tuƙuru don kare ƙasar da dimokraɗiyyarta a kowane hali.''
Masu zanga-zangar sun soki sanarwar da rundunar sojin ta fitar, kamar yadda wakilin BBC Chris Ewokor daga Abuja ya faÉ—a.
A ranar Laraba ne wasu mutane É—auke da adduna suka kai wa masu zanga-zangar hari a Abuja.
Ganau sun ce É—aruruwan masu zanga-zangar ne suka taru a yankin tsakiyar birnin a lokacin da aka kai musu harin.
Wani mai zanga-zanga ya ce daga baya an kama wasu daga cikin maharan an kuma miƙa su ga hukumomi.
An fara zanga-zangar ne sakamakon kisan wani matashi da Æ´an sandan rundunar Sars suke yi a farkon watan Oktoba.
Masu zanga-zangar sun yi kira da a rushe sashen Sars na rundunar Æ´an sandan.
Hukumar Æ´an sanda ta rufe sashen tare da sanar da buÉ—e wani sabo - mai suna SWAT.
Amma masu zanga-zangar sun yi watsi da wannan mataki, suna ganin cewa sauyin bai isa ba a matsayin yi wa rundunar Æ´an sandan garambawul.
Zanga-zangar ta jawo hankalin mutane da dama a faɗin duniya, inda a baya-bayan nan ma shugaban Tuwita Jack Dorsey ya wallafa saƙo a shafin yana mai goyon bayan zanga-zangar.