Ministan kwadagon najeria yace an kashe direbar sa a zanga-zangar rushe SARS.

 An kashe direban ministan Æ™wadagon Najeriya a zanga-zangar EndSars

An kashe direban ministan ƙwadagon Najeriya, Fetus Keyamo a zanga-zangar EndSars a jiya Laraba a Abuja.

A wani sakon Twitter da ya wallafa ministan ya ce, an kashe direbarsa Mr. Yohanna Shankuk, bayan ya ajiye mota sakamakon datse titi da masu zanga-zanga suka yi, sai ya yi kokarin takawa da ƙafa zuwa ofishinsa.



Mutane da dama ne suka jikkata a zanga-zangar ta EndSars bayan wasu matasa dauke da makamai sun afkawa gungun mutanen da ke gangami akan titi.

Hotuna da bidiyo da aka yaɗa a shafukan zumunta sun nuna yadda matasan suka ɓullo daga wani wuri daban ɗauke da sanduna suna kai wa masu zanga-zangar hari.

Ƙungiyar kare haƙƙi ta Amnesty International ta yi zargin cewa wasu ne suka ɗauki nauyin matasan domin tarwatsa zanga-zangar.

Kazalika, sun farfasa gilasan motoci kuma an ji wa wasu mummunan rauni.

Kusan mako guda kenan ana yin zanga-zanga a wasu jihohin Najeriya domin neman yin gyara ga ayyukan ƴan sanda a ƙasar.


Post a Comment

Your comment will be directly sent to the website developer.

Previous Post Next Post