Hukumar zaɓe a Guinea ta ce shugaban ƙasar Alpha Conde ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar ranar Lahadin da ta gabata.
Alƙalumman sakamakon zaɓen ya nuna Mista Conde mai shekara 82 ya samu kashi 59 na yawan ƙuri'u a zaɓen mai cike da ƙalubale.
Babban abokin hamayyarsa Cellou Dalein Diallo wanda ya yi ikirarin lashe zaɓen kafin sanar sakamako ya samu kashi 33 na yawan ƙuri'u.
Hakan na nufin Alpha Conde zai yi wa'adin mulki na uku.
Mr Diallo, 68, won 33.5% of the ballots, the electoral commission said.
"We are still going to refer the matter to the constitutional court, without having too many expectations," Mr Diallo told Agence France-Presse.
Sabon tsarin mulkin da masu zabe suka aminta da samar wa a watan Maris ya ba Shugaba Conde damar neman karin shekaru karagar mulkin kasar.
Sabon kundin tsarin mulki bai yi watsi da wa'adin shugabanci biyu ba, amma ya sake tsara matakin, don haka yawan wa'adin da aka yi a baya ba su cikin lissafi.
Mutane da dama ne aka kashe a watannin da aka shafe ana zanga-zanga bayan Mista Conde ya ayyana kudirinsa na neman wa'adin mulki na uku.
Babbar mai shigar da ƙara ta kotun hukunta laifukan yaki a duniya ICC, Fatou Bensouda, ta yi gargdin cewa waɗanda suka aikata laifi ko tunzura jama'a a rikicin zaben na Guinea za su fuskanci hukunci.