An saka dokar hana fita jahar taraba

Gwamnatin Jihar Taraba ta saka dokar hana fita a Jalingo Gwamnatin Jihar Taraba ta saka dokar hana fita a Jalingo babban birnin jihar biyo bayan wawashe wurin ajiyar kayan abinci da matasa suka yi. Mataimakin Gwamna Alhaji Haruna Manu ne ya sanar da dokar a daren Asabar yayin wani jawabi ga al'ummar jihar. Manu ya koka kan yadda matasan suka ɓalle wuraren ajiyar sannan suka yashe kayan da aka tanada domin tallafa wa mabuƙata. "Saboda haka gwamnati ta saka dokar hana fita daga ƙarfe 11:00 na daren Asabar zuwa 8:00 na safiyar Litinin," in ji mataimakin gwamnan. Ita ma gwamnatin Jihar Kaduna ta saka irin wannan dokar saboda yashe wuraren ajiyar kayan abincin da dubban matasa suka yi. Dokar ta Kaduna wadda ta fara aiki a yammacin Asabar, ta awa 24 ce kuma za ta yi aiki ne a dukkanin ƙananan hukumomin jihar. Tun farko an fara saka dokar ne a Jihar Filato, inda aka ga dubban matasa a Jos na ɗibar kayan abincin da aka ajiye domin bayar da su a matsayin tallafin annobar korona.

Post a Comment

Your comment will be directly sent to the website developer.

Previous Post Next Post