Hukumomi a Ivory Coast sun tabbatar da kisan mutun 11 kusan mako daya kafin zaben shugaban kasa.
Rikicin zaben mai nasaba da kabilanci ya faru ne a garin Dabou.
Yan sanda sun tabbatar da kama sama da mutun 50 dauke da makamai.
A ranar Litinin ne fada ya fara barkewa tsakanin yan kabilar Adjoukrou da ke goyon bayan dan takara a jam'iyyar adawa, da kuma yan kabilar Dioula da ke goyon bayan shugaba mai ci Alassane Ouattara.
Masu adawa na ci gaba da kira ga yan kasar da su kauracewa babban zabe da za'a yi a karshen wata, inda shugaba Alassane Outtara ke neman tazarce a wa'adi na uku.
A baya Alassane Outtara ya ce ba zai tsaya takara ba, to amma daga baya ya canza shawara.
Sama da mutun 1,000 ne a ka kashe a rikicin da ya biyo bayan zaben shugaban kasa a Ivory Coast na shekarar 2010.
Rikicin ya zo ne bayan da tsohon shugaba Lauren Gbagbo ya ki sauka daga mulki, a lokacin da ya sha kaye a hannun shugaba mai ci Alassane Ouattara.