'yan boko haram sun gamu da ajalin su yayin wani artabu a jahar Yobe

An kashe ɗan sanda da 'yan Boko Haram shida a Yobe Wani ɗan sanda da kuma mayaƙan ƙungiyar Boko haram shida sun rasa rayukansu yayin wata fafatawa a Jihar Yobe. Kakakin "Yan Sandan Jihar Yobe, Dungus Abdulkarim, ya tabbatar wa da Kafar kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN faruwar lamarin a jiya Asabar. Lamarin ya faru ne a Babban Gida biyo bayan harin da 'yan bindigar suka kai a cikin motoci ƙirar Toyota Hilux guda huɗu da misalin ƙarfe 4:00 na yammacin Asabar. Garin Babban Gida yana da nisan kilomita 50 daga Damaturu, babban birnin jihar. Wakilin kafar talabijin ta Channels ya ga dakarun sojan Najeriya na yunƙurin fita domin tunkarar maharan. Kazalika, rahotanni sun ce an cinna wa wasu ɓangarori na ofishin 'yan sandan yankin wuta da kuma wani sansanin sojoji.

Post a Comment

Your comment will be directly sent to the website developer.

Previous Post Next Post