Yariman Saudiyya Turki Al-Faisal ya caccaki
Isra’ila
Yariman Saudiyya Turki Al-Faisal bin Abdulziz al-
Saud, kuma tsohon shugaban hukumar leƙen asirin
Æ™asar ya caccaki Isra’ila inda ya kira ta babbar mai
mulkin mallaka da ke amfani da ƙarfi da rusa
matsugunin FalasÉ—inawa.
Yarima Turki al Faisal ya yi waÉ—annan kalaman ne a
wani taron tsaro ta intanet da Bahrain ke jagoranta
a Manama a ranar Lahadi wanda ya samu halartar
ministan harakokin wajen Isra’ila Gabi Ashkenazi
wanda ya yi watsi da kalaman.
Al-Faisal ya Æ™ara da cewa “Isra’ila tana rusa gidaje
yadda ta ga dama kuma tana kashe duk wanda
take so.”
Amma a martaninsa, ministan harakokin wajen
Isra’ila ya ce ya tausayawa kalaman da suka fito
daga yariman.
Ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa “zargin karya
da jami’in Saudiyya ya yi a taron Manama ba ya
nuna gaskiya ko asalin canjin da yankin ke ciki."
View more on Twitter
Zafafan kalaman da suka fito daga Yarima Turki al
Faisal a wajen taron Manama ya nuna girman
ƙalubalen duk wata yarjejeniya da ake son cimma
tsakanin Æ™asashen Larabawa da Isra’ila muddin
babu batun cin gashin kan Faladinawa.
Kuma wannan na faruwa ne a yayin da manyan
ƙasashen Larabawa kamar Bahrain da Daular
Larabawa suka yi maraba da Isra’ila a wajen taron
bayan daidaita hulÉ—arsu da Isra’ila da gwamnatin
Trump ta jagoranta.