Daular larabawa ta ce tana fuskantar hare-hare ta
intanet bayan Æ™ulla alaÆ™a da Isra’ila
Gwamnatin HaÉ—aÉ—É—iyar Daular Larabawa ta ce ta fi
fuskantar hare-hare ta intanet bayan ƙulla alaƙar da
ta yi da Isra’ila a watan Satumba.
Muhammad Hamad al-Kuwaiti babban jami’in kula
da tsaro ta Intanet na Daular Larabawa ne ya
bayyana haka a Dubai a wani taron tsaro da
ƙasashen yankin ke gudanarwa.
Ya ce Æ™ulla alaÆ™a da Æ™asarsa ta yi da Isra’ila ya jefa
HaÉ—aÉ—É—iyar Daular Larabawa cikin fuskantar
barazanar daga mahara.
Sai dai jami’in bai yi cikakken bayani ba game da
hare-haren, ko an gano masu kutsen.