Mutumin, wanda ya bar gida yana da shekara 26 zuwa ci-rani a kudancin Najeriya, ya koma mahaifarsa bayan da ya tsufa sosai. Katin ɗan ƙasarsa ya nuna cewa yana da shekaru 73 a duniya.
Malam Sa'idu Abdullahi ya ce ya daɗe yana burin komowa gida cikin danginsa da ya bari tun kafin a bai wa Najeriya 'yancin kai.Kazalika jikokin 'yan uwansa suke ganin kakansu mai labarin al'ajabi da ba su taɓa ganin shi ba, sakamakon shafe tsawon zamani wajen ci-rani a garin Ibadan. Ɗaukacin 'yan uwa da dangin Malam Sa'idu Abdullahi sun mance da shi saboda sun ɗauka tuntuni Allah ya yi masa cikawa.ya bar gida ne yana kan ganiyar samartaka a zamanin Sarkin Kano Abdullahi Bayero, kaka ga Sarkin Kano Aminu Ado Bayero wato tsakanin shekarar 1926 zuwa 1953.
Idan haka ne, zai iya kai wa shekaru 95 ko kusan haka a duniya.
Ya ce a wancan lokaci ya tafi kudancin Najeriya ne domin fadada sana'ar sayar da goro. Sannan wani babban dalili shi ne, ya kuduri aniyar tafiya neman wani kawunsa da ke bin mahaifiyarsa yana da shekara 26 ne ya yi masa ƙaimin barin gida.
Wani abin mamaki game da Sa'idu Abdullahi shi ne duk da shafe gwamman shekaru a kudancin Najeriya, harshensa bai juye ba, kuma tsufa bai hana shi gane al'amuran rayuwa ba. Ko da yake, shekaru sun fara taɓa masa ƙafa.
Ɗumbin mutanen wannan yanki ne ke ci gaba da dafifin zuwa ganin Malam Sa'idu Abdullahi, dattijon da ya bar ƙauyensu Damau tun yana ƙarƙashin turawan mulkin mallaka, kafin a san za a ƙirƙiri jihar Kano, yanzu dai ya komo cike da farin cikin cewa ko ba komai ya dawo gida cikin 'yanci da gatansa.