Yan tawaye sun kashe mutum 21 a Jamhuriyyar Dimokraɗiyyar Congo.

'Yan tawaye sun kashe mutum 21 a Jamhuriyyar Dimokraɗiyyar Congo
Jami'ai a Jamhuriyyar Dimokraɗiyyar Congo, sun bayyana cewa 'yan tawaye sun kashe aƙalla mutum 21 a gabashin ƙasar. Ana zargin ƙungiyar Allied Democratic Forces wato ADF ce ta kai hari ga abokan hamayyarta kafin ta kai hari a ƙauyen Lisasa da ke yankin Beni a arewacin lardin Kivu. 'Yan tawayen sun ƙona wurare da kuma lalata wani asibiti. Ko a wannan makon sai da aka dora alhakin wani hari da aka kai kan ƙungiyar ta ADF wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 15. Ƙungiyar ta kashe ɗaruruwan mutane a hare-haren ramuwar gayya tun bayan da rundunar sojin Congo ta kaddamar da yaƙi da su a bara.

Post a Comment

Your comment will be directly sent to the website developer.

Previous Post Next Post